Dattijan Askira Sun Koka Kan Makomar 'Yayan su Mata 14 Da Suka BAce A Wani Harin Kwanton Bauna.

Sojojin Najeriya.

'Yan binidga da ake kyautata zaton cewa 'yan Boko Haram ne suka kai harin ranar 20 ga wata Yuni kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa.

Iyayen wasu mata 14 daga karamar hukumar Askira a jahar Barno, sun koka kan yadda hukumomi basu ce musu komi kan makomar ‘yayansu, wadanda suka bace tun bayan wani harin kwanton bauna da ake zargin ‘yan binidigar Boko Haram suka kai kan ayarin motocin rakiyar wata gawa. Lamarin dai ya auku ne kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa, ranar 20 ga watan Yuni.

Kakakin dattijan Askira inda iyayen matan suke da zama, Barrister Madu Bukar, wanda yayi magana da manema labarai kan wannan batu, ya bayyana damuwa da bakin cikin da iyaye da sauran al’umma suke ciki tun aukuwar lamarin.

Kukan iyayen kuwa yazo ne a kuma dai dai lokacin da kungiyar ta Boko Haram ta saki wani fefen vidiyo inda mata 14 suka gabatar da kansu suna neman gwamnati tayi musayar fursunoni, makamancin wadda aka yi tsakanin ‘yan bindigar da ya kai ga sakin wasu ‘yan matan makarantar Chibok da Boko Haram din tayi garkuwa da su na tsawon shekaru.

Wakilin Sashen Hausa Haruna Dauda Biu, wanda ya kalli fefen vidiyon da kungiyar ta saki- ta hanun Sahara Reporters, yace wasu daga cikin matan suna kuka, yayinda suke gabatar da kansu.

Matan sun fada hanun ‘yan binidgar ne lokacin da suka farwa ayarin motocin ‘Yansanda, wadanda suke raka gawar wata jami’ar ‘Yansanda wace za’a maida ita gida domin yi mata jana’iza a Lassa.

Your browser doesn’t support HTML5

Dattijan Askira