Gwamnatin ta kuma fada cewa rashin na'u'rorin gwajin shinkafar sabanin yadda ake dasu a bakin teku yana cikin dalilan hana shigowa da shinkafa.
Dalili na biyu shi ne dakatar da shigowa da makamai kasar domin kawar da ta'addanci da ya addabi kasar musamman a yankin arewa maso gabas da kuma fashi da makami tare da yin garkuwa da mutane.
Tun kemfen din 2015 jami'an gwamnati suke karfafa hadin kai da kasashe makwafta domin magance matsalar ta'addanci.
Ministan harkokin cikin gida na yanzu Janar Abdulrahaman Dambazau wanda yake cikin kwamitin kemfen din ya hango lamarin. Yana mai cewa magana ce da bata Najeriya ba ce kawai. Ta shafi kasashen dake makwaftaka da bangaren arewa maso gabas irin su Kamaru, Chadi da Nijar. Yace magana ce ta ta'addanci domin kafin makaman su kawo Najeriya suna bin ta wasu kasashe.
Dalili ke nan da kasashen suka kafa rundunar tsaro ta hadin gwuiwa mai hedkwata a Ndjemina babban birnin Chadi da nufin yiwa duk wani aikin ta'addanci kofar rago.
Hukumar hana fasakwauri ta Najeriya a watan jiya ta gano wasu bindigogi masu saukin sarafawa dari shida da aka shigo dasu ta teku lamarin da ake gani zai yi nasara a iyakokin kasa.
Tsohon kwanturolan hukumar na Katsina Gidado Bala Muhammad ya bayyana yadda suke arangama da 'yan fasakwauri da kan shigo da haramtattun kaya da makamai. Yace dama shi mai fasakwauri da gaske yake fitowa sai an yi shiri za'a iya cin nasara a kansa. Dan fasakwauri babu abun da baya iya yi da makamin da yake rike dashi.
Dr. Sani Yakubu Gombe dake koyaswa a yankin arewa maso gabas ya yaba daukan matakai masu tsauri kan iyaka. Yace idan kana san ka karya lagon dan ta'adda ka hanashi abinci da makamai. Amma a wancan lokacin 'yan Boko Haram suna samun abinci da makamai. Yanzu matsin da aka yi ya karya lagon 'yan Boko Haram.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5