A Ivory Coast, sojojin kasar da suka yi bore na kwanaki biyu cikin makon jiya, domin matsin lamba a kara musu albashi, sun cimma yarjejeniya da gwamnati ranar jumma'a, domin magance rikicin, kamar yadda wakilai daga duka sassan biyu suka yi bayani.
Jin tashin binidgogi a sansani soja dake Abidjan ya razana mazauna birnin suna zaton sojojin zasu ci gaba da boren ne, amma cikin daren jiya rahotanni suka ce an cimma daidaito a Bouake, birni na biyu a girma a kasar, inda kuma nan ne boren ya samo asali.
Sojojin suna neman a biya ko wannensu dala dubu 20, amma saje Mammadou kone, wanda ya wakilci masu boren, ya gayawa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa, gwamnati zata biya su sefa milyan biyar ranar Litinin, saura kuma a rika basu kaso kaso kan albashinsu.
Sakamkon boren ne shugaba Allasane Ouattara, ya sallami babban hafsan hafsoshin kasar, da speto janar na 'Yansanda da kuma kwamadan rundunar jendarmari.