Ivanka Trump Ta Kai Gangamin Bunkasa Tattalin Arzikin Mata Ivory Coast

Ivanka Trump a wata masana'antar mata

'Yar shugaban kasar Amurka, kuma mai bashi shawarwari kan tattalin arziki ta sanar da wani shirin Amurka na bunkasa tattalin arzikin mata da za a rika zuba jari kai tsaye a kamfanonin da mata je jagoranta.

‘Yar shugaban Amurka Donald Trump kuma mai bada shawara a fadar White House Ivanka, tana kan hanyarta zuwa kasar Ivory Coast a ci gaba da ziyarar kwanaki hudu, da zummar habbaka harkokin kasuwancin mata a yankin Afrika ta Yamma

Ivanka Trump da take baiwa mahaifinta sahawara a kan tattalin arziki, ta fara yada zango ne a babban birnin kasar Habasha Addis Ababa a ziyararta ta Afrika da ta fara a ranar Lahadi, inda ta sanar da wasu shirye shiryen miliyoyin daloli da gwamnatin Amurka zata taimakawa mata masu kasuwanci

A jiya Litinin Ivanka Trump da David Bohingian mukaddashin shugaban hukumar saka jari a kasashen waje (OPIC a takaice suka sanar da wannan shirin da ake kira "2X Afrika", da zai samar da dalan Amurka biliyan daya da kuma saka jarin dala miliyan 350 kai tsaye a kamfanoni da gidaniyoyi da mata suka mallaka ko suke jagoranci, wanda zasu yi aiki mai inganci ga ci gaban mata a matsayin kasa da kasa a cikin Afrika.

Da yammacin ranar Lahadin, Ivanka Trump ta gana da shugaban Habasha Sahle-Work Zewde, inda suka tattauna kan batun sauyi a Afrika da zai kai ga kara ba mata dama a nahiyar.

Ta kuma tatttuan batun ci gaban mata da firai ministan kasar Abiy Ahmed, inda ta yaba masa a kan kara yawan mata dake rike muhimman mukamai a gwamnatinsa.