Italy Ta Yi Allah Wadai Da Kalaman Macron Na Kushe Ta

Shugaban Faransa, President Emmanuel Macron

Kasar Italiya ta gayyaci jakadar Faransa a yau Laraba a wani matakin mayar da martani ga kalaman shugaban Faransa Emmanuel Macron inda ya kushewa gwamnatin Italiya sibili da korar daruruwar bakin haure da aka ceto a cikin jirgin ruwa.

Macron ya ce dokokin kasa da kasa sun bukaci Italiya ta karbi bakin hauren wadanda galibinsu sun fito ne daga kasashen Afrika dake kudu da sahara.

Bisa ga cewar mai magana da yawun gwamnati Benjamin Griveaux, Macron ya fadawa jami'an gwamnatinsa cewa, "gwamnatin Italy ta nuna matukar halin son kai da rashin Imani game da halin kuncin da bil'adama ya shiga".

Ministan harkokin cikin gida na Italiya Matteo Salvini ya fada a yau Laraba cewa, itama Faransa ta karbi bakin haure kana Macron ya daina fada da baki ya yi aiki da abin da yake fadi.

Wannan takaddamar ta bayyana matsalolin da kasashen nahiyar Turai ke fama da su wurin kula da harkokin bakin haure. Yayin da Italiya ta karbi bakin haure sama da dubu dari 640 tun shekaru biyar da suka shude, sauran kasashen kungiyar tarayyar Turai sun yi watsi da kirar da Rome din take yi su karbi bakin haure.