Yau Alhamis kasar Isra'la ta ce ta kaddamar da hare haren sama kan dakarun Iran a cikin Syriya cikin dar, inda ta ce martani ne ga harin rokoki da dakarun Iran suka kaiwa dakarunta a tuddan Golan.
Dakarun Isra'ila sun ce sun maida hankali ne a hare haren da aka kai da jiragen sama kan cibiyoyin ayyukan leken asiri, cibiyoyin da ake ajiyar makamai da motocin yaki, kuma jiragen sun tarwatsa na'urorin da Syria ke amfani dasu domin kariya.
Isra'ila ta kuma yi gargadin cewa, ba zata bari barazanar Iran ta sami wurin zama a syriya ba, kuma ta ce zata dorawa gwamnatin Syriya alhakin duk abubuwan dake faruwa a iyakokinta ba.
Ministan tsaro Avigdor Lieberman ya shaidawa wani taron jami'an tsaro ya shaidawa wani taron harkokin tsaro cewa, Harin da Isra'ila ta kai ya ruguza kusan dukkan kayyakin aiki a Syriya .'' yace, inna fatan mun rufe wannan babin kuma kowa sun fahimta.
A lokutan baya, Isra'ila bata magana a kan ayyukanta na soji a Syria inda akea kyautata zaton ta kai hare haren jiragen sama da dama kan dakarun kasar Iran.