Isra'ila Ta Fara Daukar Matakan Korar 'Yan Gudun Hijira Da Masu Neman Mafaka Daga Afirka

'Yan Afirka na zanga-zangar matakan da Isra'ila ke dauka na korar 'yan gudun hiijira da masu neman mafaka karfi da yaji zuwa kasashensu na asali

Isra’ila tana daukar matakan korar dubban bakin haure na Afrika zuwa kasashensu. Bayanin yana kunshe ne a rahoton da wakilin Muryar Amurka Robert Berger ya aiko daga birnin Kudus.

Hukumomin kula da bakin haure na kasar Irsa’ila sun fara bada takardun korar masu neman mafaka daga kasashen da suke fama da yake-yake kamar Eritrea da Sudan. Wannan ne matakin da Isra’ila ta dauka na baya bayan nan, na korar bakin haure kimamin dubu arba’in daga kasashen Afrika da suka shiga kasar ta barauniyar hanya cikin shekaru goma.

Wani mutum da ya bayyana kansa da Michael ya samu takarda ya bar kasar. Takardar na cewa, nan da ranar daya ga watan Afrilu ya bar kasar zuwa Afrika, wanda ake gani daga Rwanda yake.

Michael yace ba daidai ba ne Isra’ila ta kori yan gudun hijira da suke neman mafaka, ganin hadarin da suke huskanta a kasashensu a Akfrika wand aka iya kaisu ga mutuwa.

Amma ita gwamnatin Isra’ila tayi watsi da ikirarin yan gudun hijiran, tana cewa akasarinsu bakin haure ne da suka bar kasashensu don neman arziki.

Takardar korar ta basu wa’adi. Bakin haure zasu iya karbar dala dubu uku da dari biyar su bar kasar dan kansu ko kuma su fuskanci hukuncin dauri. Jami’an Isar’ila sun ce yan Afrika suna barazana ga kasar na Yahudawa kuma suna zarginsu da yawan aikata laifi da kuma lalata rayuwa a yankin birnin Tel Aviv ta Kudu.

Wani dan kasar ta Isra’ila dake zaune a Tel Aviv ta Kudu, Mai Golan yace tilas bakin hauren su tafi.