Isra'ila Na Ci Gaba Da Kakkausar Sukar Amurka

Isra'ila tana ci gaba da kakkausar sukar da take yiwa Amurka dangane shawarar da hukumomi a Washington suka dauka na kin hawa kujerar naki kan kudurin da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri'a a kai, wand a ya bukaci Isra'ila ta daina gine gine a yankunan 'yan shrae wuri zauna a yankunan Larabawa.
Jakadan Isra'ila a Amurka Ron Dermer,ya zargi gwamnatin Obama da hada baki kan kasarsa, kan kuri'ar da aka kada makon jiya.
Dermer yace gwamnatin Isra'ila tana da "shaida sahihiya" kan take taken Amurka gameda kudurin, kuma a shirye suke su bayyanawa sabuwar gwamnatin Amurka mai jiran gado, alabarshi idan ta ga dama ta fadawa Amurkawa.
Amurka wacce take da ikon hawa kujerar naki a kwamitin sulhu, ta kauracewa jefa kuri'arta a kudurin na ranar jumma'a, wadda ya bada damar kudurin ya sami amincewa, wand a shine irinsa na farko da yayi Allah wadai da Isra'ila kan manufofinta gameda yankunan larabawa data mamaye tun 1979.