Israila da Senegal Sun Sake Kulla Huldar Diflomasiya

Shugaban Limaman Senegal Imam Oumar da shugaban kasar Israila Reuven Rivlin

Haduwar Firayim Ministan Israila Benjamin Natanyahu da Shugaban kasar Senegal Mackay Sall a taron ECOWAS da aka yi a Liberia tayi sanadiyar sake hada huldar diflomasiya tsakanin kasashen biyu wadda ta wargaje bara

Israi’la da Senegal sun maido da tsohuwar huldarsu ta diflomasiyyar da ta wargaje bayanda Senegal din ta zama daya daga cikin kasashen da suka gabatarda kudurin la’antar Isra’ila a zaman da kwamitin tsaro na Majalisar Dinki Duniya ko MDD yayi a watan Disambar bara inda yayi Allah wadai da ginin gidajen Yahudawa da Isra’ila din ke yi.

Firai ministan Israila Benjamin Netanyahu ya hadu da Shugaban Senegal Macky Sall a Liberia a lokacin taron Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin kasashen Afirka ta Yamma ta ECOWAS.

Isra’ila ta ce Jakadanta zai koma Senegal, yayinda ita kuma Senegal goyi bayan baiwa isra’ila matsayin zaman ‘yar kallo a cikin zauren Kungiyar Kasashen Afrika.

A watan Disambar bara ne kasashen Senegal da New Zealand da Malaysia da Venezuela suka gabatarda kudurin da ya bukaci Isra’ila ta kawo karshen aiyukan girka gidajen da take a yankunan da ta mamaye na Falasdinu.

A kan hakan ne, Netanyahu ya koro jakadun Senegal da New Zealand daga kasarshi. Israila bata da alakar diflomasiyya da Malaysia da Venezuela.