Babban sakateren hukumar kula da Kiristoci masu zuwa kasar Isra'ila aikin ibada na jihar Adamawa Bishop Jinga Mayo yace yarjejeniyar ta biyo bayan shimfidar da hukumar ta yi inda aka baiwa mutane dari da aka zabo daga kananan hukumomi 21 cikin 500,000 da suka je aikin ibada horo kan sabbin fasahohin noman rani.
Ana saran inji babban sakataren hukumar, kowannensu zai koyawa mutane goma daga karamar hukumar da ya fito abubuwan da ya koya.
Dr, Yusuf Hayatu malami a kwalajin koyar da aikin noma dake Ganye na daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin ya ce fasahar da suka koya na noman tumaturin rani da damina zai habaka sana'ar da rage irin asarar da ake samu wajen nomansa musamman lokacin damina.
'Ba su boye mana asirin kiwo ba' inji Mrs, Felicia Nzomi Shaki wadda ta ce tuni sun kara kungiyoyin gama kai don tabbatar da shirin ya isa ga sauran manoman karkara.
Kawo yanzu an soma shirin a kananan hukumomi bakwai da kwalejin koyon sana'ar noma na Ganye.
Saurari Karin bayanin rahoton Sanusi Adamu.
Your browser doesn’t support HTML5