Isra’ila Da Hamas Sun Kulla Yarjejeniyar Tsagaita Wuta

Falasdinawa suna murnar kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Kulla wannan yarjejeniya na zuwa ne yayin da yakin na Isra'ila da Hamas ya haura wata 15 da barkewa.

Hamas da Isra’ila sun kulla yarjejeniyar tsagaita wuta wacce za ta da sakin “wasu” daga cikin mutanen da kungiyar mayakan take tsare da su fiye da shekara guda, kamar yadda masu shiga tsakani da jami’an Amurka suka bayyana a ranar Laraba.

Shugaban Kwamitin Hulda da Kasashen Waje a Majalisar Dattijai ta Amurka, Sanata Jim Risch ne ya bayyana labarin yayin wani zama na tantance Sanata Marco Rubio, wanda zababben Shugaba Donald Trump ya zaba don zama sakataren harkokin waje.

Masu zanga zanra neman a saki mutanen da Hamas ta kama a Tel Aviv

Yayin bayyana labarin, Risch ya kuma yi kira da a yi taka-tsantsan.

“Kafin mu fara murna gaba daya, tabbas dukkanninmu za mu so ganin yadda za a aiwatar da hakan,” in ji shi.

Labarin ya samu karbuwa daga bangarori daban-daban na jam’iyyu siyasar Amurka, inda Sanata Chris Murphy na Connecticut, daga jam’iyyar Democrat, ya mayar da martani ga Risch da cewa, “wannan tabbas labari ne mai kyau.”