Kungiyar ISIS ta saki wani fefe da take ikirarin sako ne daga shugabanta Abu Bakr al-Baghdadi, mutumin da aka juma ba’a ganshi a bainar jama'aba ko aka ji daga gareshi na tsawon watanni.
Sakon ya bukaci musulmi da su tashi suyi yaki a madadin kungiyar kuma suyi hijira zuwa yankin kasashen Syria da Iraqi data kama ta ayyana a zaman "daular Islama".
Yace "musulmai basu da wata hujja na kin daukar makamai na kare kungiyar" a yakin da ta ke yi.
Kafofin yada labarai na yammacin duniya sun gaza tantance ko muriyar ta al-Baghdadi ce.
al-Baghdadi ya bada sako na karshe da muryarsa cikin watan Nuwamban bara, kwanaki bayan da jami'an kasar Iraqi suka ce an jikkatashi a wani farmaki da jiragen yaki da aka kai kan wani gari dake kusa da kan iyakar kasar da Syria.
A ranar Laraba ma'aikatar tsaron Iraqi ta bada labarin cewa wani farmaki da jiragen yakin kasashen da suke taron dangi a yaki da ISIS sun kashe wani mukaddashin kwamandan kungiyar ta ISIS.