Reshen Kungiyar mayakan ISIS dake Afghanistan ya dauki alhakin wani harin bam da aka kai a wajen wani bikin aure wanda yayi sanadiyar kisan akalla mutane 63 tare da jikkata wasu su 183.
Wadanda harin kunar bakin waken ya shafa a bikin da aka kwashe tsawon dare ana shagali a wani makeken daki da ya cika makil da jama’a, galibin jama’ar tsirarun ‘yan Shi’a kabilar Hazara ne.
Wani mai magana da yawun ma’aikatar cikin gidan Afghanistan, Nasrat Rahimi ya tabbatar da adadin wadanda suka mutu sakamakon harin a wata sanarwa da aka fidda da safiyar yau Lahadi. Ya kuma ce mata da yara na cikin wadanda harin ya shafa.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da harin bam din da aka kai wurin bikin a matsayin “zalunci akan ‘yan shi’ar Afghanistan, majalisar ta kuma ce ta tattara bayanan hare-hare da yawa da aka kai a baya akan ‘yan kabilar.
Jakadan Amurka a Kabul, John Bass shi ma yayi Allah Wadai da wannan harin ta shafinsa na Twitter ya na mai kiran harin a matsayin “tsananin zalunci.”