Isira'ila Ta Kai Hari Kan Wasu Kayan Yakin Iran a Siriya

  • Ibrahim Garba
A yau dinnan Litini Isira'ilar ta amsa cewa ita ta kai hare-hare kan wasu kayan yaki na Iran da ke cikin Siriya.

A wata amsa zama sanadin aukuwar abu, da Isira'ila ba ta saba yi ba, da safiyar yau dinnan Litini Isira'ilar ta amsa cewa ita ta kai hare-hare kan wasu kayan yaki na Iran da ke cikin Siriya.

Rundunar sojin Israili ta ce ta kai harin ne saboda mayakan Iran sun kadamar da harin roka daga Syria wanda su ka auna kan tuddan Golan.

Israili ta ce ta auna hare-haren jiragen saman ne kan wani kayan yaki da ke filin jirgin saman Dimashku, da kuma wuraren da Iran ke horar da mayaka da kuma tara kayan yakinta, da kuma kayan kariya daga makamai masu linzami na Siriya.