Kasar Iraq ta kaddamar da wani farmaki yau Lahadi da safe da nufin sake kwace Tal Afar, wani gari dake gabashin Mosul, daga hannun mayakan IS.
WASHINGTON D.C. —
A sanarwar da aka yayata a tashohin talabijin, Firai minister Haider al-Abadi ya shaidawa masu mamayar, “kuyi saranda ko kuwa ku mutu”.
Rundunar sojin kasar Iraq ta kiyasta cewa, kimanin mayakan IS dubu biyu ne suke mafaka a Tal Afar.
Dakatun hadin guiwa sun kara kaimin hare hare a garin kafin kai hari ta kasa, abinda ya tilastawa dubban farin kaya kauracewa garin.
Tal Afar na daya daga cikin yankuna na karshe a Iraq da har yanzu yake karkashin ikon mayakan IS, bayan kwace birnin Mosul dake tazarar kilomita tamanin da babban birnin kasar, a watan Yuli.
Ba kamar Mosul ba, galibin wadanda ke garin ‘yan Sunni ne. Ana kyautata zaton, mayakan Shiya zasu yi tasiri a neman ikon Tal Afar da ya kasance gida ga ‘yan Shiya da dama.