Kotun dake shari'ar lamuran ta'addanci a Baghdad ta yankewa wasu mata 'yan asalin Rasha su 19 hukumcin daurin rai da rai saboda shiga kungiyar ISIS kazalika ta daure wasu daga kasashen yankin tsohuwar tarayyar Rasha ranar Lahadi akan laifin
WASHINGTON DC —
A Iraqi, wata kotun kasar ta yanke wa wasu mata 'yan kasar Rasha su 19 daurin rai da rai saboda an same su da laifin shiga kungiyar ISIS.
Babbar kotu, wacce take shari'ar ta'addanci a Bagadaza,ta kuma yanke wasu mata su shida 'yan Azerbaijan, da wasu mata su hudu daga Tajikistan hukuncin na daurin rai-rai a jiya Lahadi kan wannan zargi na shiga kungiyar ta'addancin.
Galibin matan sun fadawa kotun cewa, mayakan ISIS ne suka kawo su Iraqi daga Turkiyya ba tareda amincewar su ba.
Tun a farkon watan nan, a ma'aikatar harkokin wajen Rasha tace akwai akalla mata masu magana da harshen Rasha da adadin su ya kama daga 50-70 wadanda ake rike da su a Iraqi, tareda 'yayan su su-fiye da dari daya.