Mai magana da yawun sojojin yace jirgin yakin Sukhoi kirar Rasha, ya sami matsalar injin ne, abinda yassa ya sako bom yayinda yake kokarin komawa mazauninsa dake wani sansanin soja.
Sakamakon faduwar bom ‘din ya lalata gidaje masu dinbin yawa da raunata a kalla mutane 11.
Anyi amfani da jirgin yakin ne a hare haren da ake kaiwa kan kungiyar IS, wanda suka kame wasu manyan bangarori a Arewa da yammacin Iraqi a shekarar da ta gabata.
Sojojin Iraqi na daga cikin kungiyar kawance da Amurka ke jagoranta wajen kai hare hare ta sama, haka kuma suna aika sojojin su domin taimakawa mayakan tsageru dake fafatawa wajen ganin sun kwato yankunan su dake hannun mayakan sakai.
Mayaka masu goyon bayan gwamnati na samun nasara, amma mayakan sa kai na rike da yankunan da suka kwace masu yawa, ciki harda wasu mayan birane.