Kwamandan Askarawan Tsaro na Musamman na juyin juya halin Iran, ya yi gargadi ga sansanonin sojin Amurka da ke yankin Gabas Ta Tsakiya cewa za su fuskanci yiwuwar harin makami mai linzami daga Iran muddun Amurka ta kakaba wa Iran sabontakunkumi.
Shugaban Amurka Donald Trump na shirin yin shela cikin 'yan kwanaki masu zuwa cewa Iran ba ta kiyaye yarjajjeniyar kasa da kasar da aka cimma a 2015 na dakile shirin makamin nukiliyarta, to amma zai baiwa Majalisar Dokokin Amurka din wa'adin kwanaki 60 don yanke shawarar ko a kakaba ma Iran sabbin takunkumi ko a'a.
Sai dai kuma kafafen yada labaran Iran sun ruwaito Kwamandan Askarawan Tsaron kasar, Mohammad Ali Jafari na gargadi jiya Lahadi cewa muddun aka kakaba masu sabbin takunkumi, to sai dai ko Amurka ta kawar da sansanonin sojinta zuwa da'irin nisan kilomita 2,000 da makamai masu linzami na Iran ke iya kaiwa.
Sansanonin sojin Amurka din na kasashen Bahrain da Iraq da Oman da Afghanistan ne, wadanda dukkansu ba su wuje nisan kilomita 500 daga kan iyakar Iran ba.