A yau Alhamis ne kasar Iran ta sanar da shirin sanya takunkumai akan wasu Amurkawa da kamfanoni guda 9 don maida murtanin abinda ta kira “saba ka’ida wadda ba za ta yarda da ita ba, saboda shawarar da Amnurka ta yanke ta sanya sabbin takunkumai masu nasaba da shirin makami mai linzamen Iran”
Sanarwar ma’aikatar harkokin wajen Iran ta ce wadannan takunkuman sun keta hakkin bil’adama kasancewa suna da alaka ta kai-tsaye ko a kaikaice da laifuffukan da gwamnatin Isra’ila ta aikata a yankunan Palasdinu ko ta hanyar goyon bayan ‘yan ta’adda. Sanarwar ta kuma ce za a bayyana sunayen mutanen da kamfanonin nan ba da dadewa ba.
Ma'aikatar Baitulmanin Amurka ta sanar da sanya sabbin takunkumai jiya Laraba akan wasu jami’an ma’aikatar tsaron Iran guda 2, da wani kamfanin a Iran, da kuma wasu mambobin wata kungiya mai mazauni a China.