Kasar Iran ta harba makamai masu linzami fiye da dozin guda kan akalla sansanonin sojin saman Iraki da sojojin Amurka ke zaune, a cewar ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon.
Mai magana da yawun Pentagon ya ce a bayyane yake an harba makaman ne daga kasar Iran.
Ya zuwa yanzu dai babu tabbacin mutum nawa aka kashe, amma Pentagon ta ce tana aiki wajen tantance yawan barnar da aka yi.
Kai hare-hare da rokoki irin wannan abu ne da aka saba gani a Iraki, wanda hakan salo ne na ‘yan bindigar da Iran ke marawa baya a yankin.
Sansanin al-Asad dai yana lardin Anbar, a baya ya taba zama cibiyar mayakan ‘yan ta’adda, yanki ne da kungiyar ISIS ta taba kwace ikon manyan birane irin su Fallujah da Ramadi da dai sauran wasu garuruwa, kuma har yanzu ta na samun goyon baya.
Babu wata kungiyar da ta fito ta dauki alhakin hare-haren, amma kamfanin dillancin labaru na AP ya bayar da rahotan cewa gidan talabijin mallakar kasar Iran ya ce kasar ta kaddamar da wasu hare-haren makamai kan sansanonin sojin.