Shugaban Iran Hassan Rouhani ne ya bada sanarwar haka lokacind a yake magana ta talabijin jiya Laraba. Haka nan kotun kasa da kasan ita ta tabbatar da cewa Iran ta shigar da karar ranar Talata.
A cikin watan Afrilu ne kotun kolin Amurka ta yanke hukuncin cewa za'a yi amfani da kudaden wajen biyan diyya ga wadanda harin bam da aka kai kan barikin sojojin Amurka a Lebanon a shekarar 1983 da ya rutsa da su, da kuma wasu hare-hare da aka dangantasu da Iran.
Iran ta musanta cewa tana da hannu a harin, daga nan tayi watsi da hukuncin kotun ta bayyana shi a zaman sata.
Ahalinda ake ciki kuma, wata mace 'yar asalin Iran, wacce ahalin yanzu kuma 'yar Birtaniya ce da hukumomin Iran suka tsare, yanzu mahukuntan kasar suna tuhumarta da yunkurin hambare gwamnatin kasar.