Iran ta kakkabo wani jirgin saman Amurka mara matuki a wani lamari da jami’an kasar su ka ce ya faru a sararin samaniyar yankin Iran amma jami’an Amurka sun ce a wani sararin samaniyar kasa-da-kasa lamarin ya auku.
Mai magana da yawun rundunar dakarun Amurka Kyaftin Bill Urban ya fada a yau Alhamis cewa wani makami mai linzame da aka harba daga kasa ne ya kakkabo jirgin na Amurka dake gewayar abubuwan dake faruwa a wani yankin kasa-da-kasa dake Hormuz.
Ya ce Amurka ba tayi wani abu na tsokana da ya janyo harin akan jirgin leken asirin ta ba, ya kuma ce ana amfani da jirgin mara matuki don leken asiri ne, da sa ido akan abubuwan dake faruwa a gabobin teku da ta saman tekun.
A bayanin da Iran ta bada, dakaru na musamman da ke sararin samaniyar kudancin lardin Hormozgan, a kusa da tekun Hormuz ne suka kakkabo jirgin.