A yau Asabar kasar Iran ta aiwatar da kisa kan wani dan jarida da ya taba tserewa daga kasar saboda aikinsa a yanar gizo wanda ya taimaka wajen kwadaita zanga-zangar yanayin tattalin arzikin kasar ta gama gari da aka yi a shekarar 2017, a cewar hukumomi, ‘yan watanni bayan da ya koma Tehran a cikin wani yanayi mai sarkakiya.
A watan Yuni ne wata kotu ta yanke wa Zam hukuncin kisa, ta na mai cewa ya aikata laifin gurbata al’umma, laifin da yawancin lokuta ya ke hadawa da leken asiri ko yunkurin hambarar da gwamnatin Iran.
Shafin yanar gizon Zam mai suna AmadNews da wata tashar kallo da ya kirkira ta manhajar tura sakonin Telegram sun yada lokutan da aka yi zanga-zangar da kuma wasu bayanan ban kunya game da jami’an da kai tsaye suka kalubalanci tsarin Shi’ar Iran.
Zanga-zangar, da aka fara a karshen shekarar 2017, ta zama babban kalubale ga gwamnatin Iran tun bayan gwagwarmayar da aka yi a shekarar 2009 a kasar.