Da yawa daga cikin ‘Yan majalisar dokokin Amurka daga jam’iyyar Republican da wasu ‘yan Democrat da ma wasu shuwagabanni kamar Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu basu amince da matsayar Obama ba, akan wannan yarjejeniya. Idan ba’a manta ba, an cimma ta ne tsakanin kasashen da suka fi karfi a duniya a birnin Vienna Talatar nan da ta gabata. Obama ya nuna cewa wannan lamari zai toshe duka wasu hanyoyin Iran na mallakar makamin Nukiliya.
A tattaunawa da yayi da kamfanin jaridar New York Times, Mr. Obama yace yarjejeniyar ta cimma muhimmiyar bukata, da masu adawa ma suka amince akai, wato cewa bai kamata Iran ta mallaki makamin Nukiliya ba.
Obama yace “Wannan shine dama mafi inganci da muka samu, ba kawai na shekaru 10 ba, amma na shekaru masu zuwa. Mun yi tanadin tawagar bincike da zata tabbatar ba su mallaki makamin Nukiliya ba”. Obama ya kara da cewa “Wannan yana da matukar daraja ta fannin tsaron kasar, da tsaron Isra’ila da wasu kawayenmu a wannan yanki. Kuma za’a kiyaye yiwuwar gasar mallakar makaman Nukiliya a wannan yanki”.
Mr. Obama yace duk wanda ya kasance shugaban kasa nan da shekaru 10 ko 15 masu zuwa, to yana da wannan dama na amfani da karfin soji ko kakaba sababbin takunkumai, amma yarjejeniyar zata bada karin haske ne akan shirin nukiliyar Iran, da kuma bada kwararan hujjoji da zai baiwa kasa da kasa shaidun daukar matakai idan aka keta yarjejeniya.