IPMAN Ta Bayyana Dalilan Karancin Man Fetur

Cunkoson motoci da babura wurin sayen man fetur

Duk da cewa gwamnatin tarayya ta biya dillalan man fetur kudin tallafin da suke binta zunzurutun kudi har nera biliyan 413 amma har yanzu jama'a na shan wuya kafin su samu mai kuma su sayeshi da dan karen tsada, to ko menen ya janyo hakan?

Shugaban dillalan man Fetur ya gayawa Muryar Amurka cewa akwai dalilai da dama da suka kawo karancin man.

Matsala ta farko babu isasshen man a wurin da suke zuwa daukoshi. Duk depo na NNPC babu mai kuma basa aiki. Matatun mai basa aiki hatta wadda take Kaduna. Aikin da ta keyi bai kai kashi goma ba.

Yanzu sun dogara ne ga depo depo na 'yan kasuwa masu zaman kansu. Su ma basu da isasshen mai. Sun biya a basu mai amma har yanzu ba'a basu ba duka da cewa sun biya da tsada. Sun biya nera 91 ko 92 akan kowace lita.

Ana sayar da mai da tsada a gidajen mai saboda sun sayo da tsada. Amma ita hukumar dake kula da yadda ake sayar da man sai tace dole a sayar akan farashin gwamnati ko kuma su rufe gidan man.

Idan sun je daukan mai bisa kaida su yi kwana biyu ko uku a yi masu lodi su tashi amma yanzu sai sun yi kwana talatin ko fiye da haka kafin su samu mai su dauka.

Ban da haka dillalan man sun ce sun biya NNPC fiye da nera tiriliyon daya. Babu kudin kuma babu man.

Inji shugaban IPMAN mafita daya ce. Gwamnati ta dubi lamarin da idon rahama.Wata shawara da shugaban ya bayar ita ce na kyale 'yan kasuwa su cigaba da harakar mai da kansu. Ya bada misali da man diesel wanda 'yan kasuwa ne ke shigo dashi. Babu hannun gwamnati saboda haka ya wadatu a farashe kasa da abun da gwamnati ta yanke. Ya kara da kiran gwamnati ta cire tallafinta.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

IPMAN Ta Bayyana Dalilan da Suka Haddasa Karancin Man Fetur - 4' 36"