Kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan dake kasar Italiya, ta sanya farashin fam miliyan 68 kan dan wasanta Mauro Icardi, wanda Real Madrid ta dade tana muradin ganin ta sayeshi sai dai abun yaci tura a farkon kakar wasan bana.
Dan wasan, Icardi ya shafe sama da wata guda ba ya bugawa Inter Milan wasa, saboda wata takaddama da ta taso tsakanin sa da kungiyar, kan wasu batutuwa, abin da ya sa kungiyar ta karbe matsayin jagoran 'yan wasan ta (Captain) da ta bashi.
Kungiyar Real Madrid ta tuntubi Inter Milan akan amincewa da biyan farashin da zarar an kawo karshen kakar wasa na bana.
kungiyar ta Real Madrid yanzu ta tashi haikan wajen ganin ta saye 'yan wasan don karfafa sashen ta na 'yan wasan gaba masu jefa kwallo, tun bayan da ta dawo da Zidane a matsayin mai horas da kungiyar bayan ta sallami kocinta Solari a makon da ya gabata.
An ruwaito cewar Shugaban kungiyar ta Real Madrid, Florentino Perez ya ware makudan kudade domin sayen sababbin ‘yan wasa a kokarin da
kungiyar ta ke yi na dawo da martabar ta a kakar wasa mai zuwa.
Tun bayan da dan wasan gaban ta Cristiano Ronaldo ya bar kungiyar ta Real Madrid, inda ya koma Juventus har yanzu kungiyar ta rasa wanda zai maye mata gurbin sa.