Inter Milan ta lallasa Borussia Dortmund da ci 2-0 a wasan cin kopin zakarun Turai na UEFA Champions League da yammacin jiya Laraba a kasar Italiya inda Milan ta dauki bakwancin wasan.
WASHINGTON DC —
Masu sharhi a kan wasannin kwallon kafa sun kwatanta wasan Milan da Dortmund da karambata, wanda ya dauke hankali a wasannin zakarun Turai na UEFA a wannan mako.
Kwallayen da aka zura a kowane zagayen wasan an same su ne ta kafafun Lautaro Martinez da Antonio Candreva kuma wannan nasarar farko da Inter Milan mai inkiya Nerazzurri tayi a wannan shekara.
Dan wasan gaba na kasar Ghana Kwadwo Asamoah mai wasansa a Inter Milan ya taka leda kuma ya taka muhimmiyar rawa a wannan nasara da Inter Milan tayi na ci biyu da nema a kan Dortmund da yammacin jiya Laraba.
Dan wasan Ghanan ya yi wasa tsawon sa’o’I tamani kafin aka sauya aka kawo Biraghi yam aye masa.