Yanzu haka Injiniyoyi da masana kimiyyar fasahar kwamfutoci na duba yadda zasu zana gine-gine tare da fasahar da za ta kare mutane. Sabbin hanyoyin da ake dubawa sun hada da samar da kofofi masu yawa da wuraren buya da kuma samar da fasahar da za ta iya matsar da bango idan bukatar hakan ta taso.
Amma kafin a fara aikin samar da wannan fasaha, dole ne sai masu bincike sun duba yadda halaiyar mutane take lokacin da suke cikin gine-gine.
Halaiyar da za a duba kuwa sun hada da yadda mutane suke da zarar sunji labarin ana harbi a ginin da suke. Shin halaiyar mutanen za ta canza idan da an tsara ginin ta wata hanya ta daban? Fasahar Virtual Reality itace matakin farko da zata amsa wannan tambayoyin, ta kuma taimakawa injiniyoyin wajen samar da gine-gine mafi aminci a cewar mataimakin farfesa a jami’ar USC, Gale Lucas.
Samar da wannan fasaha za ta taimaka wajen tabbatar da aminci a gine-gine lokutan da hare-haren ‘yan bindiga, wadanda ke haddasa asarar rayukan mutane masu yawa musamman a Amurka.