A wata ganawa ta wuni guda da sashen hulda da farar hula na shedikwatar rundunar sojin Najeriya ta yi da manema labarai a Jos, fadar jihar Filato, rundunar sojin ta ce tana gudanar da ayyuka da suke shafar rayuwar jama’a ta hanyar samar da ruwan sha, gina makarantu bada magunguna da duba lafiyar al’umma kyauta duk don kara dankon zumunci da fahimtar juna.
Shugaban sashen hulda da farar hula na rundunar sojin Najeriya, Manjo Janar Markus Kangye, ya ce manufar taron da ‘yan jarida a karo na biyu a wannan shekara, shine su bayyana gaskiyar yadda suke gudanar da aikinsu ba kamar yadda ake shafa musu kashi ba, musamman a kafafen sada zumunta na zamani.
Shima shugaban wurin hutawa na manyan sojoji dake kwalejin tsaro ta Najeriya, Dakta Tsini Tsitsi Kuabe, ya ce taron ya kara fahintar da al’umma matakan da za su bi ko da sun sami rashin fahimta da jami’an soji.
Malam Yakubu Taddy, daraktan labarai da al’amuran yau da kullum na tashar rediyo da talabijin mallakar jihar Filato, cewa ya yi a wasu lokuta rashin samun bayanai a kan lokaci daga jami’an tsaro, shike janyo hasashe da labaran karya.
Shugaban kungiyar ‘yan jarida mata a jihar Filato, Madam Nene Dung, ta ce sun fahimci cewa akwai ka’ida kan yadda sojoji ke gudanar da aikinsu.
Taron da aka yi wa lakabin “muhimmacin ‘yan jarida wajen magance matsalolin tsaro” ya kuma tattauna kan yadda ‘yan jarida za su yi iya kokarinsu wajen hadin kan kasa da tabbatar da zaman lafiya.
Domin karin bayani ga rahotan Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5