INEC: 'Yan Siyasa A Guji Kalaman Batanci, Ko Zargi Mara Tushe

A jihar Bauchi hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC tayi zama da masu ruwa da tsaki musamman shugabannin, 'yan siyasa domin fadakardasu muhimmanci gudanar da zaben gwamnoni, da na 'yan majalisun dokoki a ranar Asabar 9 ga wannan watan cikin lumana da kwanciyar hankali.

A zaman taron, shugabannin jam’iyun siyasar sun bayyana damuwarsu, da kuma irin barazanar da suke fuskanta da suka hada da zargin sojan gona, da karerayin da ake yadawa a kafafin sadarwa na zumunta dake bayanin nuna goyon baya ga wasu 'yan takara ko kuma jam’iyya.

Shugaban hukumar zabe a jihar Bauchi Farfesa Ibrahim Abdullahi, yace irin korafe-korafen da shugabannin siyasa suka gabatar masa, sun hada da batun yin zabe batare da naurar tantance masu kada kuri’a, da kuma sha’anin tsaro.

A nashi bayanin shugaban jam’iyyar APC a jihar Uba Ahmed Nana, yayi zargin cewa akwai wasu jam’iyyu dake hayan sojojin gona dauke da alamun tambarin jam’iyyar APC domin aikata mummunan aiki.

Dan takarar kujerar gwamna a zaben da za ayi a ranar Asabar karkashin tutar PRP Farfesa Ali Pateh ya musanta rade radin dake ba zuwa cewa wai ya janye takarar da ya keyi.

Shima dai shugaban jam’iyyar NNPP a jihar Bauchi mai alamar kayan dadi Injiniya Muhammed Barde ya nisanta jam’iyyar sa da irin bayanan da ake yadawa a kafar sada zumunta.

Ga rahoton wakilin shashen Hausa na Muryar Amurka Abdulwahab Muhammad.

Your browser doesn’t support HTML5

INEC: 'Yan Siyasa A Guji Kalaman Batanci, Ko Zargi Mara Tushe 2'30"