INEC Ta Tsayar Da Ranar Da Za a Sake Zabuka a Najeriya

Hukumar INEC Ta Yi Taron Manema Labarai Bayan Dage Zabe

A Najeriya hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta tsayar da ranar Asabar 23 ga wannan watan Maris, amatsayin ranar da za a sake zabubbuka a wasu rumfunan zabe da aka samu matsaloli a wasu yankunan kananan hukumomi na jihohi biyar.

Tuni dai hukumar zaben ta fara tura muhimmam kayan aikin zabe zuwa wuraren da za a sake zaben.

Jihohin da za a sake zaben kuwa sun hada da Bauchi da Benue da Kano da Filato da kuma Sokoto.

A jihohin da za a sake zaben sun hada da kananan hukumomi guda goma sha biyar dake da jamilar masu kada kuri’a sama da dubu 22.

Mallam Ahmed Waziri Zadawa, shine shugaban sashen wayar da al’umma da hulda da jama’a a hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Bauchi, ya yi ‘karin haske game da shirin zaben na ranar Asabar.

Wani shugaban al’umma, Alhaji Sagir Madakin Shira, ya bukaci manyan yan takaran kujerar gwamnan jihar Bauchi da su guje wa dukkan wani abin da zai kawo rashin kwanciyar hankala a jihar Bauchi.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Abdulwahab Muhammad.

Your browser doesn’t support HTML5

INEC Ta Tsayar Da Ranar Da Za a Sake Zabuka a Najeriya - 3'30"