Ranar Asabar mai zuwa wato 14 ga wannan watan Yuli ranar ce da za'a gudanar da zaben gwamnan jihar Ekiti.
Hukumar zaben Nigeria, wato INEC ta bakin sakatarenta na aiwatar da mulkin hukumar Dr Musliu Omoleke ya ce sun shirya tsaf su gudanar da zaben. Ya ce sun raba kayan aiki zuwa duka kananan hukumomi 16 dake jihar kana sun horas da ma'aikatan wucin gadi sana da dubu 11 wadanda zasu yi ayyukan zaben. Za'a yi zaben ne a mazabu 2195.
Dr Omoleke ya bada tabbacin cewa hukumar zaben ba zata yi mitsitsi a zaben ba. Ya kuma umurci jama'a su zabi wanda suke so domin hukumar zata yi sahihin zabe.
Babban sifeton 'yan sandan Nigeria Ibrahim Idris ta bakin mataimakin kwamishanan 'yan sandan Mr.Abayomi Shogunle ya ce 'yan sanda ba zasu mara wa kowa baya ba amma zasu yi aikin tabbatar da tsaro. 'Yansanda zasu tsaya kan gaskiya. 'Yan sanda zasu kare kowa tare da kuri'unsu domin su yi tasiri a zaben.Babban sifeton ya sha alwashin koran duk wani dan sanda da aka samu da hannu cikin siyasa, wato ya bar aikinsa ya shiga harkar siyasa.
Shugabannin APC da na PDP sun ce sun shirya wa zaben ranar Asabar.
Kawo yanzu jami'an 'yan sanda sama da dubu 30 aka jibge a jihar ta Ekiti domin tabbatar da tsaro lokacin zaben.
A saurari rahoton Hassan Umaru Tambuwal
Your browser doesn’t support HTML5