Shugaban hukumar zaben Najeriya Prof. Mahmud Yakubu, ya ce hukumar sa ta duba duk lamuran da suka faru ta kuma dage zaben ranar Asabar 16 ga wata ba da katsalandan na kowa ba.
Jama'a da dama a Najeriya na ta raderadin cewa an yi wa hukumar shisshigi ne aka rinjayeta ta dage zaben, amma hukumar ta INEC ta musanta zargin.
Yayin da yake magana wani taron manema labarai kan dage zaben na 2019, Prof. Yakubu, ya ce hukumarsa ta dau alhakin dage zaben 100 bisa 100
Da a ka tambaye shi ko hukumar za ta bukaci karin kudi don gudanar da zaben a Asabar mai zuwa?.
Farfesa Yakubu, ya amsa da hukumar ba za ta yi korafi kan haka ba.
Wannan dai na faruwa ne a daidai lokacin da mutane ke muhawara ta bangarori daban-daban, na nuna yadda dage zaben ya maida hannun agogo baya da wasu zarge-zarge da ba wata hujja da a ka bayyana da za ta iya amfani da ita.
Muhammad Murtala na kungiyar tallafawa kamfen din Buhari (BSO) ya ce dage zaben ba zai shafi hasashen samun nasararsu ba.
Shi kuma shugaban babbar jam’iyyar adawa na arewa maso yammacin Najeriya, Ibrahim Kazaure, ya yi zargin da ma APC ba ta son a gudanar da zaben ne.
Hukumar zabe kan nanata cewa ita mai zaman kan ta ne kuma duk wanda ya lashe zabe kuri’ar jama’a ce ta kawo shi kan kujera.
Saurari rahoton Nasiru Adamu El Hikaya daga Abuja:
Your browser doesn’t support HTML5