INEC Ta Bude Zauren Karbar Sakamakon Zabe a Abuja

Shugaban INEC Ya Gana Da Shugabani Da Daraktocin Hukumar Zaben Kasa

Hukumar zaben Najeriya ta bude dakin karba da gabatar da sakamkon zaben shugaban kasa a hukumance daga dakin taro na kasa da kasa da ke Abuja.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmud Yakubu ya bude dandalin sauraron sakamakon da bayyana cewa jami’an kawo sakamakon daga jihohi na kan hanyar shigowa Abuja don haka za a dakatar da fara fadar sakamakon zuwa karfe 11 na yau Litinin.

Haka nan shugaban ya fadi dokokin shiga dakin sauraron sakamakon da su ka hada da samun shaidar tantancewa ta izinin shiga.

Kwamishinan wayar da kan masu kada kuri’a, Muhammad Haruna ya yi bayanai kan kalubale da matakan da hukumar ta dauka kan sassan da a ka samu rikici ko rashin tsaro da ya kawo akasi a lamuran zaben.

Da alamun sakamakon zaben na karshe zai iya kai wa Talata ko zuwa sanyin safiyar Laraba in an kwatanta da yadda lamarin ya kasance a 2015.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El Hikaya:

Your browser doesn’t support HTML5

INEC Ta Bude Zauren Karbar Sakamakon Zabe a Abuja - 2'29"