INEC Ta Bayyana Fargabar Tsaro A Aikin Rijistar Masu Zabe Da Za Ta Soma A Najeriya

  • Murtala Sanyinna

INEC

A yayin da take shirye-shiryen soma aikin sabunta rijistar zabe, hukumar Zaben Najeriya INEC, ta bayyana fargaba kan sha’anin tsaro.

Hukumar zaben Najriya INEC, ta tsara soma aikin rijistar masu jefa kuri’a a fadin kasar a ranar Litinin mai zuwa, to amma kuma ta bayyana fargaba akan tsaron ma’aikata 5,346 da ta tsara za su gudanar da aikin.

Yayin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa, shugaban hukumar zaben Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce yanzu haka hukumar ta kammala dukan shirye-shiryen soma aikin, haka kuma ta tanadi dukan na’urorin da take bukata na gudanar da aikin.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu (Instagram/inecnigeria)

Yakubu ya kuma bayyana kudurin hukumar na tabbatar da cewa ba wani dan Najeriya da ya isa jefa kuri’a da za’a bari baya a wannan aikin a duk fadin kasar.

To sai dai kuma ya ambato hare-hare na baya-bayan nan da aka kai wa ofisoshin hukumar a wasu sassan kasar, wadanda ya bayyana a zaman wani yunkuri na kassara kudurin hukumar na aiwatar da ayukanta.

Shugaban hukumar ya ce duk da yake hare-haren sun dan ragu a ‘yan kwanakin nan, to amma akwai fargabar irin barazanar da yanayin tabarbarewar tsaron kan iya haifarwa ga jami’an da za su yi aikin rijistar, da ma jama’ar da ake yi wa rijistar zaben.

Farfesa Yakubu ya ce sakamakon damuwar da hukumar ta ke ciki, ta aike da korafe-korafen ta ga gwamnatin tarayya, haka kuma ta tattauna da hukumomin tsaro da dukkan masu ruwa da tsaki da ma jam’iyyun siyasa, domin tabbatar da aikin ya sami nasara.

Yadda Aka Gudanar Da Zabe a Jihar Kano

Ya ce “mun tattauna akan tsare-tsaren mu da kuma damuwarmu. Dukan masu ruwa da tsaki sun yi muwafaka akan cewa wajibi ne hukumar ta baiwa tsaron rayukan jama’ar da ake wa rijista da jami’an rijistar muhimmanci, da kuma tabbatar da tsaron kayayyakin aikin da suke da tsadar gaske.

A wannan karon dai hukumar ta INEC ta fito da wani sabon salo, inda ta soma gudanar da rijistar zabe ta yanar gizo tun daga ranar 19 ga watan nan na Yuni, kafin soma aikin rijistar a dukan rumfunan rijista 2,673 a fadin kasar.