Masu fashin baki a kasar Indiya sun ce ba lallai bane wannan mataki yasa Pakistan ta daina ba wa kungiyoyin 'yan ta'adda, irinsu Hizbul Mujahiddin da suke cin Karensu ba babbaka a yankin Kashmir tudun mun tsira ba.
An rufe bakin zaton na Indiya akan Washington da wani dan gajeren bayani daga Karamin Minista biyo bayan rubutun twitter da Shugaba Trump yayi na sabuwar shekara da cewa, "Pakistan bata biya Amurka da komai ba na tallafin da ta bata a baya ba sai karya da yaudara".
Kamar yadda Jitendra Singh yace, “Ya nuna karara tare da watsar da matsayar Indiya akan yadda ta’addanci yake, kuma kamar yadda Pakistan ke da hannu a cikin kulle-kullen ta’addanci ya kunsa.”
Arvind Gupta, Daraktan Kungiyar Binciken Vivekananda International Foundation a New Delhi yace, “gaggawa ce idan aka zargi abinda Shugaba Donald Trump zai iya yi, amma yanayin sabo ne”.