India Ta Soke 'Yan Cin Gashin Kan Yankin Kashmir

Amit Shah, ya fadawa majalisar kasar yau Litinin cewa shugaban kasar ya saka hannu akan wata doka da ta soke kudiri na 370 da ya bai wa jihar dama ta yi dokokinta kuma take da iko akan duk wasu al’amura

A wani mataki da ta yanke, gwamantin India ta masu tsananin kishin kasa ta ‘yan Hindu, ta soke ‘yan cin gashin kai na musamman da ta ba yankin Kashmir a shekaru da dama da suka gabata, wanda hakan ya janyo fargaba na abin da zai biyo baya a yankinta da shi kadai ne Musulmai suka fi rinjaye.

Sa’o’i kadan bayan da aka jibge jami’an tsaro a cikin Jihar, Ministan cikin gidan kasar, Amit Shah, ya fadawa majalisar kasar a yau Litinin cewa shugaban kasar ya saka hannu akan wata doka da ta soke kudiri na dari 370 da ya bai wa yankin dama ta yi dokokinta kuma take da iko akan duk wasu al’amura in ban da harkokin kasashen waje, tsaro da kuma sadarwa.

Sannan kuma dokar ta hana duk wani dan kasar ta India daga wajen jihar daga zama a yankin na dindindin, da siyan fili da kuma rike wani mukami a yankin.

A cikin wata sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Wajan Pakistan ta fitar, ta yi “Allah wadai” da matakan da India ta dauka “akan yankin da kasashen duniya suka amince da ake takaddama” akansa.