Haramta wasan harbi da ake shirye-shiryen yi cikin gasar kasashen da suke Commonwealth, hakan zai sanya kasar India ta kauracewa shiga wasannin motsa jiki, na kasashen kungiyar Commonwealth da za'ayi a shekarar 2022 a Birmingham.
Kasar ta India dai itace ta zama zakara a gasar harbi a shekarar bara cikin gasar wasannin motsa jiki na Commonwealth, wace kasar Australia ta karbi
bakoncin sa, inda kasar India ta lashe lambobin yabo 16, wanda suka hada da Zinare 7.
Kasar ta samu jimilar lashe lambobin yabo guda 66, da wannan nasarar da ta samu ta kasance kasa ta uku mafi kwazo bayan kammala gasar.
A watan Yuni data gabata ne kwamitin da ke tsara wasannin ya bayyana shirinsa na soke gasar harbi cikin gasar ta 2022.
Sakamakin hakanne kasar India ta ce zai kawo mata mumunar koma baya, kan nasarorin ta na lashe adadin lambobin yabo masu yawa, don haka tayi barazanar kaurace wa shiga gasar muddin aka haramta yin wasan harbin.
Sai dai hukumar shirya gasar tace za tayi zama akan wannan batu da India take barazana akan sa.