Ana kula da mutane fiye da 30 da suka sami raunuka a wani karamin asibiti, yayin da kuma aka shiga bincike kan musabbabin hatsarin, a cewar wani jami’in a ofishin ‘yan sanda na Nashik, kimanin kilomita 190 daga Mumbai, babban birnin kasuwanci na Indiya.
Kafafen yada labaran kasar sun ruwaito cewa, motar ta kama da wuta ne bayan ta daki watan tankar man diesel. Wasu hotunan bidiyo da aka saka a kafafen sada zumunta sun nuna yadda motar take nutse a cikin manyan harsasan wuta.
Prime Minista Narendra Modi ya fada a shafinsa na twitter cewa “Hatsarin motar safa a Nashik ya taba mu matuka. Ina jajantawa wadanda suka rasa ‘yan uwansu a hatsarin.” Ya kara da cewa za’a bai wa iyalan kowane mutum da ya rasa ran sa dalar Amurka 2,400, wadanda suka sami raunuka kuma dala 600 ko wannensu.
Modi yayi addu’ar samun waraka cikin sauri ga wadanda suka jikkata, yana mai cewa hukumomin yankin suna samar da dukkan taimako da wadanda lamarin ya shafa suke bukata.