Inda rabin kudin man fetur din Najeriya suka shige

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Matatar man fetur din Najeriya ta tara dala biliyan takwas amma rabinsu kadai ne suka shiga asusun gwamnati. Sannan an sace kudin man fetur da suka kai dala biliyan arba’in, kwatankwacin kasafin kudin shekara biyu na gwamnatin tarayya.

Game da biyo bayan cece-ku-cen maganar almundahana da dukiyar kasa ta bangaren ma’aikatun gwamnati. An sami fallasa maganar kudaden matatar man fetur ta Najeriya ta tara kudin da yawansu ya kai fiye da Dalar Amurka miliyan Dubu Takwas.

Idan aka canza jimillar kudin da aka wawashe din a Nairar Najeriya ya kai Naira biliyan dubu takwas. To amma matsalar itace an saka abinda bai fi rabin wannan kudi bane kawai a asusun gwamnatin tarayya.

Abokin aikinmu Aliyu Mustapha Sokoto yayi hira da wani masanin tattalin arziki daga Jami’ar Abuja Dakta Nazif Abdullahi Darma game da wannan matsala da ta taso. Inda yayi tsokaci akan lamarin. A ganinsa in ba dawo da wadannan kudade aka yi ba to ba a sami canjin da ake zato ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Inda rabin kudin man fetur din Najeriya suka shige - 2'19''