Ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014 ce 'yan Boko Haram suka sace 'yan makaranta fiye da dari biyu da hamsin a makarantar 'yan mata dake garin Chibok cikin jihar Borno.
Tun daga lokacin da aka sacesu har yau da suka cika watanni tara a tsare babu duriyarsu ko kamaninsu. Saidai a baya can sojojin Najeriya sun yi ikirarin gano inda yaran suke saidai wai suna son su bi lamarin cikin ruwan sanyi su kubutosu.
Akwai ma wani lokacin da kakakin sojojin Najeriya Manjo Janaral Chris Olu Kolade yace sun kubutar da duk yaran sai dai wasu guda takwas. Amma daga bisani ya janye sanarwar domin babu kashin gaskiya ciki.
Matan gwamnonin arewa bakwai a karkashin jagorancin Mrs Dooshima Suswan matar gwamnan jihar Binuwai suka ziyarci jihar Borno sabili da halin da jihar ke ciki har da lamarin 'yan matan Chibok din. Sauran matan da suke cikin tawagarta su ne matan gwamnonin Adamawa, Taraba, Neja, Kaduna, Kogi da Nasarawa. Sun bada tallafin kayan abinci ga al'ummar jihar Borno wadanda rikicin Boko Haram ya daidaita.
Madam Suswan tace sun kai ziyarar ce domin jajantawa gwamnati da al'ummar jihar Borno da ma sauran jihohin arewa maso gabashin Najeriyan kan irin asarar rayukan da aka yi sakamakon rigingimun.
Madam Suswan tace lamarin 'yan matan Chibok babban bala'i ne a kasar. Tace har yanzu yana nan sabo a zuciyarsu domin tun lokacin da lamarin ya faru basu dakatar da yi masu addu'a ba..
Madam Suswan ta kira iyaye kada su bari abun da ya faru a Chibok ya sa su hana 'ya'yansu mata shiga makarantu domin ilimi shi ne gimshikin rayuwar dan Adam..
Shi ma gwamnan jihar Borno Kashim Shettima yace 'yan Boko Haram sun sace yara da mata da dama kuma wadanda suka sace a makarantar Chibok har yanzu lamarin na damunsu kuma ba zasu yi kasa a gwiwa ba wajen ganin cewa an cigaba da bunkasa ilimi a jihar.
Gwamnan ya yabawa matan gwamnonin kan jajircewa da suka yi na ziyartar jihar Bornon ganin cewa kwana kwanan nan aka kai hari a garin Baga amma sai gashi harin bai karya masu gwiwa ba na kin ziyartar jihar.
Akan 'yan matan Chibok din wakilin Muryar Amurka ya tambayi Sanata Ali Ndume wanda yake wakiltar yakin kudancin Borno da ya hada da garin Chibok. Yace tun da aka sace 'yan matan yana magana a kai. Gwamnatin Borno tana magana a kai kuma suna yin duk abun da yakamata su yi. Amma yace yakamata gwamnati ta dage ta gaya masu abun da zasu iya gayawa iyayen yaran. Yau wata tara gwamnati bata basu labarin da zai kwantar masu da hankali ba.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5