kamar yadda muka ji ra'ayoyin samari daban daban akan wannan bakuwar dabi'a ta kai 'yan mata kanti ko shopping a turance, wannan karon dandalin voa ya sami bakuncin dattijiya kuma uwa malama Salma Yusuf wadda ta yi mana jawabi da kuma bada shawarwari ga matasa.
Malamar ta bayyana cewar kwaikwayo da son yin abubuwan zamani yasa jama'a da dama sun fita haiyacin su musamman na kauce ma al'adun su na asali wadanda addinin da al'adar su suka amince masu yi.
Tarbiyya irin ta Hausawa bata bada damamr saurayi ya fita zuwa ko'ina da budurwa ba tunda bata riga ta zama matarsa ba, dan haka idan ma wata kyauta saurayi yake son ba budurwar sa, kamata yayi ya aika wa iyayenta su bata har gida ba daukar ta su tafi wani wuri ba.
Jama'a da dama sun fuskanci matsaloli da dama kuma daga karshe abin ya zamar masu da na sani, dan haka kauce ma irin wannan dabi'a shine kawai yafi kyau, kuma iyaye su rika kulawa da tarbiyar 'ya'yan su domin kauce wa irin wannan bakuwar dabi'a.
Ga cikakkiyar hirar a nan.