Abubuwan da zaki yi ko kuma kiyaye ta fuskar rayuwar yau da kullum
Abubuwan da zaki yi ko kuma kiyaye ta fuskar rayuwar yau da kullum
- ·Kada nauyinki ya shige kima. Likitanki zai iya gaya maki nauyin da kika kara lokacin ciki.
- ·Kada ki sha taba ko giya ko kuma kiyi amfani da miyagun kwayoyi. Wannan zai iya zama da illa ga jaririnki na lokaci mai tsawo ko ma ya kai ga mutuwa. Ki nemi shawar likita kan hanyar daina shaye shaye.
- ·Idan ba likita ya hanaki ba, kiyi kokari ki motsa jiki na a kalla sa’oi biyu da rabi a mako. Zai taimaka idan kika tsara tsawon lokaci da zaki motsa jiki a mako. Idan kika rika motsa jiki a kai a kai kafin daukar ciki, zaki iya ci gaba muddar yanayin lafiyarki bai sake ba, ki kuma rika bayyanawa likita ayyukan motsa jiki da kike yi har zuwa lokacin da zaki haihu. Ki kara koyo game da yadda zaki kasance cikin koshin lafiya lokacin da kike da ciki.
- ·Kada ki yi wanka da ruwa mai yawan zafi ko kuma ki shiga cikin kwamin wanka da ruwan ke da zafi ainun ko dakin gasa jiki.
- ·Ki sami isasshen barci ki kuma nemi hanyoyin samun hutu.
- ·Ki nemi bayanai. Ki karanta littatafai, ki kalli hotunan bidiyo, ki halarci ajin koyarda batun haihuwa, ki kuma yi Magana da iyaye mata da kika sani.
- ·Ki tambayi likita dangane da azuzuwan koyarda batun haihuwa da zaki iya halarta tare da maigidanki. Azuzun zasu taimaka wajen yin shiri kafin haihuwar jaririnki.