Masu sauraronmu assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa a wannan shirin na amsoshin tambayoyinku, Da fatan masu azumi kuma ana kan ayyukan ibada lafiya.
TAMBAYA 1: Don Allah, a tambaya mana masana:- Wace kasa ce, ko kuma al'umma, ke yin mafi tsawon sa'o'in azumi, ko mafi gajartar sa’o’in azumi, a duniya?
MASU TAMBAYAR: Zakaria Salifu Gidan Rumji da Adamu Shamuwa mai Dawaki a Shikal Jamhuriyar Nijar.
TAMBAYA 2: Za kuma a ji maimaicin tambayar nan kan dalilan kasashen Mali da Burkina Faso na shirin kulla yarjejeniya da kasar RASHA, da kaurace ma kasar Faranasa; da kuma yadda al’amarin zai kasance?
MASU TAMBAYAR (Idan an tuna, su ne): Babandi Mamman Bande,
da Tasiu Unguwar Tudu, Damagaram da Issuhu Madatai, da Ali Sarkin yakin Ni'ma, da Shugaba Iliya Maishayi Garkin Daura.
AMSOSHI:
Ga amsar tambaya ta daya daga bakin Dr. Adamu Baɓikkoi, malami a Kwalejin Horas da Malamai ta Gwamnatin Tarayya dake Yola, jihar Adamawa, Najeriya.
Tambaya ta biyu kuma, dama Farfesa Prof Kamilu Fagge na Jami’ar Bayero ta Kano ne ya amsa ta.
A sha bayani lafiya:
Your browser doesn’t support HTML5
04-15-23 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU.mp3