Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya, ta kalubalanci hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke kan zaben gwamnan jihar Imo a farkon makon nan.
A ranar Talatar da ta gabata, kotun kolin karkashin jagorancin Alkalin Alkalan Najeriya, Tanko Muhammad, ta soke nasarar da gwamna Emeka Ihedioha na jam'iyyar PDP ya samu a zaben gwamnan jihar ta Imo.
Kotun ta kuma ayyana dan takarar APC, Hope Uzodinma, a matsayin wanda ya lashe zaben, wanda aka yi a watan Fabrairun 2019.
Yayin wani taron manema labarai, Shugaban Jam'iyyar ta PDP, Uche Secondus, ya ce sun yanke shawarar da a sake nazari sosai kan dukkanin al'amuran da ke kewaye da hukuncin kotun kolin.
Secondus ya kuma yi zargin cewa, sun lura; ana juya kotun kolin wacce ke karkashin Justice Tanko.
Amma daya daga cikin lauyoyin da suka kare dan takarar Jam'iyyar APC Barr. Damian Dodo, ya ce su ba su da wata damuwa da wannan hukunci.
A cewarsa, kotun koli ta yi amfani da tsarin doka ne tsantsa wajen yanke hukuncin.
Barr. Damian ya kara da cewa, alkalai 7 ne suka amince da hujjojin da aka ba kotun, saboda haka zai yi wuya a soke hukuncin.
Shi ma kwararre a harkokin zamantakewan dan Adam kuma Malami a Jami'ar Abuja Dokta Abubakar Umar Kari ya ce, wannan ne karon farko da kotun koli za ta yi irin wannan hukunci da ya bude sabon babi a harkar siyasar kasar.
Saurari cikakken rahoto cikin sauti daga Abuja:
Your browser doesn’t support HTML5