A jawabinsa na farko, Emeka Ihedioha ya shaida wa al'ummar jihar da kuma sauran jama'a da suka garzayo domin bikin cewa "Manufarmu ita ce mu sake gina Jihar Imo, mu sake fasalinta, mu kuma mayar da ita cibiyar ilimi, noma, masana'antu, yawon bude ido, al'adu, wasanni, nishadi, inganta baiwa, kimiya da fasaha, da kuma yin amfani da albarkatun kasarmu, don kirkiro damar raya tattalin arziki, da kuma inganta rayuwar al'ummarmu."
Ihedioha ya dai bayyana kudurori kimanin 15 da gwamnatinsa zata cimma a cikin shekaru hudu masu zuwa, ciki har da samar wa matasa abin yi, da tallafawa mata, da samar da stabtataccen ruwan sha, da inganta ilimi, noma, tsaro, da dai sauransu.
Sashen Hausa ya yi hira da wadansu da suka halarci bukin rantsar da sabon gwamnan. Wani mai suna Okpara na cewa, "Ina son abinda ke faruwa yau. Kenan abin da muka roka, kuma shine abin da muke ta kokarin gani, wato kubutar da jihar Imo. Muna so a dama da talaka. Kuma mun san cewa a matsayinsa na gogaggen shugaba, Emeka Ihedioha zai dawo da martabar jihar Imo."
Al’umman jihar Imo sun bayyana fatar ganin al’amura sun gyaru da kuma fatar ba za a sake komawa gidan jiya ba. Sun bayyana bukatar ganin 'ya'yansu sun samu isasshen ilmi, kuma ya zamana duk aikin da za a yi a jihar ya zama na kwarai.
Saurari cikakken rahoton Alphonsus Okoroigwe
Your browser doesn’t support HTML5