IMF: Shugabar hukumar bada lamuni ta duniya na ziyara a Najeriya

r Christine Lagarde shugabar hukumar bada lamuni ta duniya wato IMF

A karon farko tun lokacin da Najeriya ta samu sabon shugaba, shugabar hukumar bada lamuni ta duniya wato IMF tana ziyara a kasar ta tsawon kwana hudu

A lokacin ziyarar ta Chrisrine Largade zata gana da shugaban kasar Najeriya Muhammad Buhari da masana tattalin arziki game da hanyar farfado da tattalin arzikin kasar.

A can baya hukumar ta IMF ta shawarci gwamnatin Najeriya da ta rage darajar Nera tare da janye tallafin man fetur.

Alhaji Kasumu Kurfi masani kan tattalin arziki ya goyi bayan shawarar da IMF ta ba Najeriya dangane da rage darajar kudin kasar tare da cire tallafin da take bayarwa kan kudin man fetur.

Alhaji Kurfi yace shawarar tana da kyau. Yace duk wanda baya sarafa abubuwan da zai sayar a waje yace kuma zai rike darajar kudinsa to ya shiga wahala. Duk kasar da ta cigaba akwai lokacin da zata rage darajar kudinta kamar yadda China tayi yanzu domin ta sa kayanta su sake samun kwarjini a kasashen waje, wato su kasance da araha yadda mutane zasu saya. Najeriya bata sarafa komi. Mai take sayarwa kuma shi ma kudinsa ya fadi.

Idan darajar kudi yayi yana da karfi ainun mutane ba zasu sayi kayan kasar ba kana ba zasu shigo da nasu kudin ba. Wannan zai kaiga tsadar kudin waje kamar dalar Amurka .

To saidai Alhaji Aminu Gwadabe shugaban kungiyar masu sana'ar canji ya bayyana shakku game da shawarar ita hukumar IMF. A tashi fahimtar idan ka rage darajar kudin kasar kayanmu zasu yi tsada, lamarin zai shafi farashi da yawa.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

IMF: Shugabar hukumar bada lamuni ta duniya na ziyara a Najeriya - 5' 10"