Illolin da Cin Hanci da Rashawa Suka Dauke Hankalin Taron Wa'azin IZALA

Bababban sakataren IZALA na kasa a taron Sokoto

Gagarumar gudummawar da ayyukan cin hanci da rashawa suke bayarwa wajen tabarbarewar tattalin arziki da koma bayan kasashen Afirka musamman Najeriya na cikin alamuran da suka dauke hankalin babban taro na kasa da kasa da kungiyar IZALA ta gudanar a Sokoto.

A makalar da ya gabatar a wajen taron babban sakataren kungiyar ta IZALA Shaikh Kabiru Haruna Gombe yace ko baya ga harkan cin hanci da rashawa a addinance, wajibi ne hukumomi da gwamnatoci su yi yaki da mummunar dabi'ar

Yace cin hanci da rashawa na yiwa cigaban kasashe tarnaki musamman idan aka yi la'akari da abubuwan dake faruwa a Najeriya. Idan ana kokarin yadda za'a tara kudaden shiga to cin hanci da rashawa ya shigo ciki ba za'a samu ba. A Najeriya duk cin hanci da rashawa ya shiga cikin harkar kasar har tattalin arzikinta ya tabarbare.

Jama'a a taron IZALA da ya wakana a Sokoto

Kazalika cin hanci da rashawa na hana cigaba domin idan an ba mutum kwangila ya yi gini ko ya gina hanya cin hanci da rashawa zai hanashi yin aiki mai kyau. Ta haka asibitoci suka lalace. Yace idan ba'a kawar da cin hanci da rashawa ba komi lalacewa zai yi kuma kasar ba zata cigaba ba.

Ya kira shugabanni su yaki cin hanci da rashawa tsakaninsu da Allah idan da gaske suke. Baicin hakan dole a ba ma'aikata isashen albashi da duk kyautatawar da ya kamata a yi masu.

Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Illolin da Cin Hanci da Rashawa Suka Dauke Hankalin Taron Wa'azin IZALA - 2' 51"