Masharhanta kan al’amurran yau da kullum da kuma na tattalin arziki sun danganta tashin farashin kayayyakin amfani na yau da kullum musamman kayan abinci ga dogaro kan shigowa da kayan kasashen waje.
Suna masu gargadin cewa duk kasar da ta kasa biyan muhimman bukatun al’ummarta zata rinka fuskantar barazanar fatara da yumwa.
Sanin kowane a Najeriya, shekara ta 2016, an fuskanci matsalar hauhawar farashin kayayyakin amfanin yau da kullummusamman dagin cimaka.
A wani bincike da wakilin muryar Amurka, Abdulwahab Muhammad ya yi wanna yanayin da kasar ta shiga ya jawo mata faduwar darajan Naira, a yayinda a gefe guda kuma darajar dala ta karu, wanda shine kudin da ake amfanin dashi domin shogowa da kayayyakin cikin kasar
Wani malami a fanin tattalin arziki a jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, dake Bauchi, Dr. Idris Isiyaku Abdullahi Dan Wanka, yace Najeriya, ta kasance kasar da ta dogara kan kayayyakin da ake shigowa dasu daga kasashen waje yana yin da kasar ta shiga na tattalin arziki yana da nasaba da wannan.
Your browser doesn’t support HTML5