Dan wasan Paris-saint Germain Idrissa Gueye, ya bayyana farin ciki da kasancewarsa a Kulob din na PSG dake buga gasar Lig 1 na kasar Faransa.
Dan wasan dan kasar Senegal ya bayyana hakane bayan wasan da PSG ta lallasa takwararta Angers daci 4-0 a filin wasa na Parc des Princes a gasar Ligue 1, inda ya jefa kwallo daya a cikin hudu a cikin minti na 59 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
Haka kuma, ita ce kwallonsa ta farko a wannan kakar wasan ta 2019/20. Wanda hakan ya sanya kulob din karkashin jagorancin kocinta Thomas Tuchel, suka kara samun nasarar wasanni uku a jere ba tare da an dokesu ba, da hakan ne ma yasa suke jan ragamar teburin da maki 12 a wasan mako na Tara.
Dan wasan Gueye mai shekaru 23 da haihuwa wanda ya canza sheka daga kungiyar kwallon kafa na Everton dake kasar Ingila zuwa PSG, ya buga wasanni takwas kenan a sabuwar kungiyar tasa, ya ce kungiyar tasa tana da dukkannin kwarewa a kowane bangare ganin yadda suka fafata da Angers.
Ya ce haka kuma zai ci gaba da nuna kwazonsa a kungiyar. A ranar 18 ga watan Oktoban nan Paris-saint Germain, za ta kara da kungiyar kwallon kafa ta Nice cikin wasan Lig 1 na bana mako na Goma.